Home Addini Covid-19: Mutane 24,000 suka gudanar da aikin Umara

Covid-19: Mutane 24,000 suka gudanar da aikin Umara

111
0

Aƙalla mutane 24,000 ne suka gudanar da aikin Umara ba tare da an samu rahoton wanda ya kamu da cutar Covid-19 ba, tun bayan da hukumomin Saudiyya suka suka bada damar fara ibadar a ranar Asabar.

Shugabannin gudanarwar manyan masallatan Makka da Madina, sun ce an ɗauki ƙwararan matakan kiwon lafiya da na hana bazuwar cutar a tsakanin masu aikin umarar.

Mai magana da yawun hukumar gudanarwa masallatan Hani Haider ya ce don tabbatar da tsabtar masallacin Ka’aba mutum dubu huɗu aka ɗauka aiki, waɗanda suke wanke shi aƙalla sau goma a rana.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply