Home Labarai Covid-19: Mutum 1, 016 sun kamu, 1,385 sun warke a Nijeriya

Covid-19: Mutum 1, 016 sun kamu, 1,385 sun warke a Nijeriya

67
0

Hukumar kula da barkewar cutuka ta Nijeriya NCDC ta bada sanarwar mutum 1,016 da suka sake kamuwa da cutar Covid-19 a kasar.

NCDC ta fadi haka ne a shafinta na intanet a daren ranar Laraba.

Kamfanin dillancin Labarai na Nijeriya NAN, ya ruwaito cewa ya zuwa yanzu, kasar ta yi wa mutum 938,602 gwaji, tun farkon barkewar cutar a ranar 27 ga watan Fuburairu.

Hukumar NCDC, ta ce yanzu haka mutum 86,576 ne suka kamu da cutar a kasar, yayin da aka tabbatar da mutum 1,385 sun warke a kwana guda da ya wuce yayin da mutum 11 suka mutu.

Hukumar lafiyar ta ce an samu sabbub kamuwa da cutar ne a jihohi 20 na kasar da Abuja.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply