Hukumomin kiwon lafiya a jamhuriyar Nijar sun bayyana cewa an samu mutum na farko da aka gano da ya harbu da cutar Covid-19 a jihar Damagaram.
A cikin wata sanarwa da aka fitar, ta ce hukumomi sun bayyana cewa cikin sakamakon gwajin jinin da aka dauka a ranar 1 ga wannan wata na Aprilu ne ya nuna cewa mutum 22 sun harbu da cutar da suka hada maza 13 da mata 9 ciki daya a jihar Damagaram.
Kawo yanzu dai gwamnatin ta ce mutane 120 ne aka samu dauke da kwayar cutar 5 daga ciki sun rasa ransu yayin da 115 ake ci gaba da kulawa da su.
Ya zuwa yanzu dai jihohi 4 ne aka samu mutanen da suka kamu da cutar, jihohin kuwa su ne babban birnin Yamai, Maradi, Dosso da Zinder.
