Mutum 155 aka tabbatar sun ƙara kamuwa da Covid-19 yayinda 4 suka mutu a Nijeriya a alkaluman da gwamnati ta fitar a ranar Litinin din nan.
Hukumar kula da yaɗuwar cutuka ta Nijeriya NCDC, wadda ta tabbatar da haka a wani saƙon twitter a daren jiya Litinin, ta ce adadin waɗanda suka kamu da cutar ya kai 55,160 daga cikin 424,186 da aka yi wa gwajin cutar.
Hukumar ta kuma tabbatar da cewa mutane 43,231 sun warke yayin da 1061 suka mutu, tun bayan ɓarkewar cutar a Nijeriya.
