Home Coronavirus Covid-19: Karin mutune 216 sun kamu 4 sun mutu a Nijeriya

Covid-19: Karin mutune 216 sun kamu 4 sun mutu a Nijeriya

128
0

Cibiyar kula da ɓarkewar cutuka ta Nijeriya NCDC ta tabbatar da mutuwar mutane 4 tare da wasu 216 da suka kamu da cutar Covid-19 a Nijeriya.

Wani saƙon twitter da NCDC ta wallafa a daren jiya Laraba, ta ce yanzu haka mutane 54,463 aka tabbatar sun kamu da cutar daga cikin mutum 411,077 da aka yi wa gwaji.

Kawo yanzu, mutum 42,439 suka warke bayan sun kamu da cutar, 1027 sun mutu, tun bayan ɓarkewarta a faɗin ƙasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply