Home Coronavirus Covid-19: Mutum 48,092 sun warke 1,093 sun mutu a Nijeriya

Covid-19: Mutum 48,092 sun warke 1,093 sun mutu a Nijeriya

119
0

An ƙara samun mutum 131 da suka kamu da cutar Covid-19 a Nijeriya sannan biyu sun mutu.

Hukumar kula da yaɗuwar cutuka ta Nijeriya NCDC ta tabbatar da hakan a wani saƙon twitter da ta wallafa a daren ranar Alhamis.

Saƙon ya ce yanzu haka mutane 56,735 suka kamu da cutar a cikin mutane 482,321 da aka yi wa gwaji.

Daga cikin wannan adadi an sallami mutum 48,092 da suka warke yayin da 1,093 suka mutu sakamakon cutar a faɗin ƙasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply