Cibiyar kula da ɓarkewar cutuka ta Nijeriya NCDC ta tabbatar da mutum 155 sun ƙara kamuwakamu da Covid-19 a ƙasar.
Hukumar wadda ta bayyana haka a shafinta na Twitter a ranar Laraba, ta ce ya zuwa lokacin ba a samu ƙarin waɗanda cutar ta kashe ba, inda adadin ya tsaya kan 1,113.
NCDC ta ce mutum 59,738 ne jimillar waɗanda cutar ta kama a ƙasar kuma daga ciki 51,403 sun warke yayin da 1,113 suma mutu.
