Home Labarai COVID-19: NAWOJ ta tallafa wa mata masu yoyon fitsari a Sakkwato

COVID-19: NAWOJ ta tallafa wa mata masu yoyon fitsari a Sakkwato

86
0

Ma’awiyya Abubakar Sadiq

A wani mataki na ci gaba da rigakafin magance bullar cutar Corona, kungiyar mata ‘yan jarida a jihar Sakkwato ta dukufa ga samar da abinci da magungunan wanke hannu ga mata masu dauke da cutar yoyon fitsari a asibitoci da kuma masu shaguna.

A ta bakin babbar Jami’ar kungiyar Hajiya Rabi Gwadabawa tace lura da yadda mata masu cutar yoyon fitsari ke bukatar tsafta da kula da su ne ya sanya kungiyar ta samar da wadannan magunguna wanke hannu da shinkafa da suke fatan za su taimaka masu matuka dangane da halin da suke ciki.

Masu yoyon fitsarin da galibin su sun fito ne daga yankunan karkara, sun nuna jin dadin su dangane da wannan tallafi da suka samu.

Shi ma babban likitan asibitin mata da yara na Maryam Abacha da ke Sakkwato Dr. Bello Lawal ya jinina wa kungiyar mata ‘yan jarida bisa samar da tallafin ga masu cutar yoyon fitsari, inda ma ya yi kira ga masu hannu da shuni su taimaka ga samar da kayan kariya daga wannan cuta ta Corona.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply