Home Addini COVID-19: Nijar za ta bude wuraren ibada ranar Laraba

COVID-19: Nijar za ta bude wuraren ibada ranar Laraba

473
0

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta yanke shawarar bude wuraren ibada biyo bayan rufe su na tsawon makonni sakamakon cutar Covid-19 a kasar.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne ta bakin kakakin ta Abdurahaman Zakaria da ya bayyana a kafar talabajin din kasar.

A cikin sanarwar gwamnatin ta ce bayan ta zauna da shugabannin addinai da hukumomin kiwon lafiya ne ta yanke wannan shawara inda daga tace daga Larabar nan masallatai da coci-coci za su kasance a bude.

Sai dai gwamnatin ta ce dole ne a kyautata matakan rigakafin cutar Covid-19 a wuraren ibadar.

Gwamnatin ta ce ta umurci gwamnoni da shugabannin kananan hukumomin kasar da su sanya ido don ganin an yi biyayya ga matakan.

A wani ci gaban ma, gwamnatin kasar ta dauki matakin dage dokar ta baci a birnin Yamai.

Wannan mataki dai gwamnatin ta dauke shi ne sakamakon raguwar karfin cutar a kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply