Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana shirin ta na hana shige da fice tsakanin jihohin ƙasar.
Mai taimakawa shugaban Nijeriya kan kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmad, ya bayyana haka a shafin sa na Twitter, yana mai cewa Ministan yaɗa labarai Lai Mohammed ya bayyana haka.
Ya ce gwamnati na ƙoƙarin dakatar da shige da fice a tsakanin jihohi da kuma rufe tashohin mota a faɗin ƙasar.
Wannan mataki dai ya biyo bayan yadda ƙasar ke ƙara fuskantar barazanar coronavirus inda a cikin kwana takwas adadin waɗanda suka kamu da cutar ya haura daga 5 zuwa 51 tare da samun mutum guda da ya mutu.
Wannan dai ya sanya gwamnatoci suka ƙara azamar ɗaukar matakan hana yaɗuwar cutar.
