Cibiyar kula da ɓarkewar cutuka ta Nijeriya NCDC ta ce mutane 322 ne suka harbu da annobar coronavirus.
A rahotonta na daren ranar Lahadi, NCDC ta ce jimillar waɗanda suka kamu da cutar ya kai 52,227 a ƙasar.
Hukumar ta ce mutum 38,944 suka warke daga cutar, yayin da 1002 suka mutu, tun bayan ɓullar annobar a cikin watan Maris na shekarar nan.
Sabbin mutanen da suka kamu a cikin sanarwar sun fito ne daga jihohin ƙasar guda takwas da suka haɗa da Legas, Bauchi, Kaduna, Edo, Bayelsa, Ogun da kuma Oyo.
