Home Coronavirus COVID-19: Nijeriya za ta tilasta amfani da takunkumin fuska a wuraren ibada

COVID-19: Nijeriya za ta tilasta amfani da takunkumin fuska a wuraren ibada

118
0

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin yaƙi da cutar corona, Boss Mustapha ya shawarci shugabannin addinai kan su tilasta wa mabiyansu yin amfani da takunkumin fuska yayin shiga masallatai da majami’u.

Boss Mustapha ya ba da wannan shawarar ne, yayin da ya ke amsa tambayoyi a lokacin taron kwamitin yaki da corona a ranar Litinin a Abuja.

Ya ce akwai jan aiki sosai a wajen shugabannin addinai da sarakunan gargajiya kan yadda za a magance tare da dakile yaduwar wannan annoba ta corona.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply