Home Coronavirus Covid-19: NYSC ta fitar da bayanai masu cin karo da juna

Covid-19: NYSC ta fitar da bayanai masu cin karo da juna

82
0

Hukumar kula da Matasa masu yi wa ƙasa hidima NYSC ta shiga ruɗanin sahihancin rahoton ɓullar cutar Covid-19 a sansanonin horas da matasan da ke Lagos, Kano da Abuja.

A ranar Litinin ne dai shugabannin NYSC na Kano da Abuja, Hajiya Aisha Tata da Walida Isa, suka fitar da bayanan cewa an samu mutum 7 da suka kamu da cutar, 2 a Kano 5 a Abuja.

Saidai kuma Daraktar yaɗa labaran NYSC Adenike Adeyemi ta bayyana Rahotanni samun ɓullar cutar a matsayin na ƙarya, a cikin wata sanar2da ta fitar da daren ranar Litinin a Abuja.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply