Home Kasashen Ketare COVID-19: Rwanda ta fara bada tallafin abinci

COVID-19: Rwanda ta fara bada tallafin abinci

79
0

Bayan mako guda da kafa dokar hana fita a Rwanda 🇷🇼 gwamnatin ƙasar ta fara rabon kayan abinci ga mabuƙata.

Jama’ar ƙasar dai sun fara shiga mawuyacin hali saboda yadda kayan abinci suka fara ƙaranci a shaguna da kasunni.

Duk da wannan yinƙuri na gwamnati, wasu jama’ar ƙasar na cewa tallafin bai isa ba yayin da wasu ke cewa an tsallake su.

Ƙasar Rwanda dai, ita ce ƙasa ta farko da ta fara hana fita da rufe iyakokin ta a nahiyar Afirika domin yaƙi da yaɗuwar cutar coronavirus.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply