Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Covid-19: Sama da mutum 255m suka rasa aikinsu a 2020 – MDD

Covid-19: Sama da mutum 255m suka rasa aikinsu a 2020 – MDD

30
0

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce cutar coronavirus ta janyo miliyoyin jama’a sun rasa aikinsu a faɗin duniya.

Wani bincike da Hukumar Ƙwadago ta Duniya ya nuna an yi rashin kashi 8.8% na sa’o’in aiki a shekarar 2020 idan aka kwatanta da shekarar 2019.

Wannan dai ya yi daidai da rasa aikin mutum miliyan 255 ko kuma linki huɗu na waɗanda suka rasa aikinsu a lokacin da duniya ta shiga matsalar kuɗi a shekarar 2009.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce an lissafa kimanin rabin sa’o’in aikin da aka rasa ne daga sauran ma’aikatan da aka rage wa lokutan aiki, waɗanda ba a kora ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply