Home Coronavirus Covid-19: Sam Nda-Isiah ya mutu

Covid-19: Sam Nda-Isiah ya mutu

101
0

Shugaban kamfanin Jaridar Leadership Sam Nda-Isaiah ya rasu a daren ranar Juma’ar nan.

Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana hakikanin abun da ya yi silar mutuwar Sam wanda masanin haɗa magunguna ne, marubuci wanda daga bisani ya kafa kamfanin na Leadership.

Saidai wasu majiyoyi dake kusa da Marigayin sun ce, ya rasu ne a wata cibiyar killace waɗanda suka kamu da cutar Covid-19.

Marigayin wanda aka haifa a ranar ɗaya ga watan Mayun 1962, ya rasu yana da shekara 58 a duniya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply