Home Coronavirus Covid-19 ta kashe babban jami’in NYSC a Kano

Covid-19 ta kashe babban jami’in NYSC a Kano

23
0

Wani babban jami’in hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidima NYSC ya mutu sakamakon cutar Covid-19 a ranar Talata.

A kwanakin baya ne dai aka tura jami’in zuwa sansanin horas da matasan da ke Kano, a can ne kuma ya fara nuna alamun kamuwa da cutar, kafin ya mutu a ranar Talata.

Mutuwar jami’in dai ta jefa fargabar kamuwa da cutar a zukatan ma’aikatan na NYSC da sansanonin horas da matasan, musamman na Kano.

Da aka tuntubi Daraktan yada labaran hukumar NYSC Emeka Mgbemena, ya tabbatar da mutuwar, saidai ya ce ba a cikin sansanin horas da matasan ya mutu ba.

A watan Yunin bara ne dai majalisar daidaita tattalin arzikin kasar wadda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ke jagoranta, ta ba gwamnatin tarayya shawarar dakatar shirin na NYSC na tsawon shekara biyu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply