Home Kasashen Ketare Covid-19 ta kashe ministoci biyu

Covid-19 ta kashe ministoci biyu

32
0

Ministoci biyu a kasar Zimbabwe sun mutu sakamakon cutar coronavirus a cikin ƴan kwanaki, wanda hakan ya tilasta kara tsaurara matakan kulle a fadin kasar.

A yammacin ranar Jumu’a gwamnatin kasar ta bayyana cewa Ministan sufuri Joel Matiza ya mutu bayan kamuwa da cutar kwana 2 bayan kasar ta yi rashin Ministan kasashen waje Sibusiso Moyo sakamakon cutar.

Ya zuwa yanzu gwamnatin kasar ta Zimbabwe ta rasa Ministoci 4 sakamakon cutar ta Covid-19.

Mataimakin Ministan lafiya John Mangwiro ya bayyana shirin da gwamnatin kasar ke yi na kara tsaurara matakai waɗanda aka saka tun farkon watan Janairu ta hanyar hana zirga-zirga cikin dare, wanda tuni an kulle gidajen abinci, mashaya da wuraren motsa jiki.

Wadanda suka kamuda cutar a kasar ta Zimbabwe sun kai 30,523 tun bayan bullar cutar inda mutane 962 suka mutu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply