Home Coronavirus Covid-19 ta tilasta rufe majalisar dokokin Ghana

Covid-19 ta tilasta rufe majalisar dokokin Ghana

25
0

Majalisar dokokin kasar Ghana ta tafi hutun dole na kimanin makonni uku, bayan cutar Covid-19 ta dira majalisar tare da kama ‘yan majalisar tare da wasu ma’aikata.

Kakakin majalisar Alban Bagbin ya sanar da cewa ‘yan majalisar sun tafi hutu daga ranar Talata, zuwa 2 ga watan Maris, domin bada damar tsabtace majalisar da kuma kare ta daga cutuka.

Akalla ‘yan majalisa 17 da ma’aikata 151 cutar ta kama, wanda hakan ya tilasta ‘yan majalisar tsagaita zaman da suke yi.

Kasar ta tabbatar da adadin mutum 73,003 da suka kamu da cutar, 482 suka mutu yayinda sama da dubu 65,000 suka warke.

Shugaban kasar, da ke yammacin Afirka, Nana Akufo-Addo, ya haramta taruwar mutane da suka hada da jana’iza, daurin aure da tarukan shagali, yayinda iyakokin kasar suka kasance a rufe tun watan Maris na bara.

 

 

 

 

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply