Home Lafiya COVID-19: USAID za ta tallafawa Nijeriya da $7m

COVID-19: USAID za ta tallafawa Nijeriya da $7m

70
0

Hukumar bada agaji ta USAID ta ce za ta tallafawa Nijeriya da sama da Dala Miliyan $7 domin yaƙi da Covid-19.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafin ta na intanet, ta ce za a yi amfani da kuɗin ne a ɓangaren ayyukan sadarwa, ruwan sha, kare kamuwa da cutuka da kuma tsare-tsare.

Hukumar ta ce wannan tallafin kuɗi ƙari ne ga sama da Dala Biliyan $5.2 na tallafin lafiya, da Dala Biliyan $8.1 da Amirka ke ba Nijeriya sama da shekara 20 da suka gabata.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply