Home Coronavirus COVID-19: ‘Yan majalisar dokokin Madagascar 2 sun mutu

COVID-19: ‘Yan majalisar dokokin Madagascar 2 sun mutu

116
0

Shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina ya sanar cewa ‘yan majalisar dokokin kasar 2 sun mutu bayan sun kamu da cutar corona.

Kazalika, an auna 12 daga cikin ‘yan majalisar an gano suna dauke da cutar ta corona.

Rahotanni sun ce akwai mutane 2,573 da suka kamu da cutar a kasar, mutane 35 suka mutu.

Kasar Madagascar dai ce kasa daya a Nahiyar Afrika da ta ce ta samar da maganin cutar corona na gargajiya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply