Home Kasashen Ketare COVID-19: Za a fara koyar da dalibai ta manhajar WhatsApp a Nijar

COVID-19: Za a fara koyar da dalibai ta manhajar WhatsApp a Nijar

117
0

Yakuba Umaru Maigizawa

Hukumomin ilimi a jamhuriyar Nijar sun yanke shawarar fara bada ilimin boko ta manhajar WhatsApp.

A wata sanarwa da ministan ilimin makarantun kimiya da fasaha ya aike wa darakatocin jihohin kasar, ya bukace su da su kirkira dandali na WhatsApp da y hada dalibai da malamansu domin fara ba da darasun ta wannan sabuwar hanya.

To sai dai tun ba a je ko ina ba, matakin ya fara shan suka daga dalibai da iyayensu, har ma da su kansu malaman, inda suke ga kasar ba za ta iya aiwatar da wannan tsari ba da ake ga sai kasashen da suka ci gaba.

Sai dai a nata bangare, gwamnatin na ci gaba da nacewa akan matakin nata inda take cewa tuni ta yi nisa a cikin shirye-shiryen ta na rungumar wannan tsari.

Manazarta dai na nuna shakkunsu kan kasar ta Nijar da suke ga ba ta da ci gaba da za ta iya aiwatar da wannan tsari ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply