Home Coronavirus COVID-19: Za a sake rufe makarantun boko a Nijar

COVID-19: Za a sake rufe makarantun boko a Nijar

210
0

A ya yin zaman majalisar ministocinta na ranar Juma’ar nan, gwamnatin jamhuriyar Nijar ta dauki matakin rufe illahirin makarantun bokon kasar daga ranar 17 ga wannan wata na Disamba zuwa daya ga watan Janairu mai kamawa.

Gwamnatin ta ce ta dauki wannan mataki ne sakamakon sake karuwar da ake samu na masu dauke da cutar corona, inda ko sakamakon gwajin ranar 8 ga wannan wata ya nuna an samu mutum 93 sabbin kamuwa.

Ta haka ne ma yanzu gwamnatin ta ce ta dakatar da dukkan wasu taruka irin su atelier da séminaire har zuwa daidaitar lamurra.

Taron majalisar ya kara da daukar matakin tilasta saka takunkumi da ajiye ababen wanke hannu a duk ma’aikatun kasar.

A yanzu haka, ko sakamakon 11 ga watan nan ya nuna mutum 34 suka harbu da cutar, sai dai a jimilce mutane 2,160 ne aka tabbatar sun harbu da cutar cikin su 1,269 sun warke, 80 sun rasa ransu ya yin da ragowar 811 na samun kulawar likitoci.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply