Home Coronavirus Covid-19 za ta kara tsananta talauci a duniya – Buhari

Covid-19 za ta kara tsananta talauci a duniya – Buhari

192
0

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana damuwar sa kan yadda yaduwar cutar Covid-19 za ta kara munana halin talauci da talakawan duniya ke ciki.

Buhari yana Magana ne a wani sakon bidiyo da ya aike ga taron babbar majalisar dinkin duniya kan lalubo hanyoyin yaki da talauci.

A wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Femi Adeshina ya fitar, Shugaban kasar ya kuma nuna damuwar sa ganin cewa kashi 10 na yawan jama’ar duniya na rayuwa cikin tsananin talauci.

Saidai ya ce gwamnatin sa na yin dukkan mai yiwuwa wajen rage radadin talaucin da bullar cutar zai haifarwa ‘yan Nijeriya da kuma tattalin arzikin ta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply