Home Labarai Cutar amai da gudawa ta barke a Kebbi

Cutar amai da gudawa ta barke a Kebbi

113
0

Gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da barkewar cutar amai da gudawa a kananan hukumomi hudu da ke jihar.

Barkewar cutar dai nada nasaba ne da gurbatattun ruwan sama da suka mamaye galibin ruwan da mutanen yankunan karkara ke amfani da su wajen sha.

Daraktan kula da lafiyar al’umma a ma’aikatar lafiya ta jihar Kebbi Muhammad Abdullahi Babuce ne ya sanar da manema labarai hakan a Birnin Kebbi, inda yace mutane dari uku da ashirin da takwas ne suka kamu da cutar.

Kananan hukumomin kamar yadda ya ce su ne, Kalgo, Maiyama, Suru, da kuma Sakaba.

Sai dai hukumomin lafiya a jihar sun bayyana cewa za su yi iya kokarin su wajen kawar da cutar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply