Home Kasashen Ketare Cutar amai da gudawa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 7 a kasar...

Cutar amai da gudawa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 7 a kasar Somaliya

75
0

Abdullahi Garba Jani

Cutar amai da gudawa da ta barke a yankin Bakol na kudu maso yammacin kasar Somaliya ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 7 kamar yadda wani jami’i ya tabbatar.

Abdullahi Nour, mataimakin gwamnan lardin ya ce karancin tsaftataccen ruwan sha da ake da shi a yankin ne ya jaza barkewar cutar da ta yi sanadin mutuwar mutanen.

Wata majiyar jami’an lafiya ta ce an kwantar da mutane da dama a asibitoci inda suke fama da cutar gudawa.

Kamfanin dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ba da rahoton cewa sama da mutane 300,000 ne suka bar muhallan biyo bayan ambaliyar ruwa da ta wakana a mafi yawan sassan kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply