Home Lafiya Cutar farar masassara (Yellow Fever) ta bulla a Nijeriya har ta kashe...

Cutar farar masassara (Yellow Fever) ta bulla a Nijeriya har ta kashe mutum 4

86
0

Saleem Ashiru Mahuta

 

Cibiyar da ke kula da cututtuka ta Nijeriya ta tabbatar da barkewar cutar farar masassara a jihohin Ebonyi da Borno da Kano da kuma Bauchi.

Jaridar Premium Times ta ce  Babban Daraktan Cibiyar Chikwe Ihekweazu ya bayyana haka a yau Juma’a. Ya ce hukumar ta fara gano barkewar cutar tun a ranar 29 ga watan Agustan da ya gabata,

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Bauchi ta taabbatar da bullar cutar a jiharta kuma tuni aka samu labarin mutuwar wasu  dalibai 4 da suka mutu a sanadiyyar wannan cuta bayan da suka ziyarci dajin Yankari (Yankari Game Reserve) a jihar Bauchi.

Bayan haka kuma Cibiyar cututtuka  ta Nijeriya ta kuma ce akwai bayanan da ta samu da ke nuna cewa cutar ta yi barna a jihohin Borno da Kano da kuma Ebonyi.

Cutar farar masassara (Yellow Fever) dai cuta ce da sauro me dauke da kwayar cutar ke yadawa ta hanyar cizon jikin dan adam. Masana kiwon lafiya sun ce ba a kama cutar ta hanyar mu’amulla da mutane ko kuma ta hanyar saduwa ko makamancin haka.

Sai dai cutar acewar masana tana da saurin kisa. Alamomin kamuwa da ita sun hada da; sauyawar kallar idanuwa zuwa ‘yelo’ da zazzabi mai zafi da ciwon-kai da kuma ciwon jiki.

To amma abin farin ciki shi ne akwai rigakafi da idan mutum yaje aka yi masa ita sau daya to za ta kare sa daga cutar har karshen rayuwarsa.

 

Majiya: Saleem/dkura

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply