Home Lafiya Cutar Hanta: Hepatitis na yiwa Dan Adam barna, amma duniya na kau...

Cutar Hanta: Hepatitis na yiwa Dan Adam barna, amma duniya na kau da kai

78
0

Daga Saleem Ashiru Mahuta

 

A yayin da ake bikin ranar wayar da kan jama’a akan cutar Hanta ta Hepatitis rukunin B da C a ranar lahadi 28.07.2019 wata likita Remilekun Olalekun da ke Abuja babban birnin tarayyar Nijeriya, ta bukaci a mayar da hankali kan cutar Hepatitis B da C, tana mai cewa sune cututtukan da suka fi kawo matsalar ciwon dajin Hanta idan aka barsu babu magani.

Olalekun wadda ta bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ta ce jama’a da gwamnati na nuna ko-in-kula ga cutar hepatitis duk da cewa tafi HIV/AIDS da tarin TB saurin kisa.

Sai dai jami’ar kiwon lafiyar ta ce akwai rigakafi wace za ta iya ba jikin mutum kariya daga kamuwa da cutar Hepatitis B. Ta kuma ce mutum mai dauke da cutar Hepatitis C zai iya warkewa idan ya dukufa shan magani.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply