Home Lafiya Cutar kyanda na barazana a kasashe 4 na Tarayyar Turai

Cutar kyanda na barazana a kasashe 4 na Tarayyar Turai

68
0

Abdullahi Garba Jani/dkura

 

An samu bullar cutar kyanda sau 90,000 a watanni shida da shigowa wannan shekara ta 2019 a wasu kasashen nahiyar Turai.

 

Babban jami’in kula da lafiya na kasar Jamus Guenter Pfaff ne ya sanar da hakan a lokacin da ya jagoranci kwamitin hukumar kula da lafiya ta duniya WHO a birnin Geneva.

 

Rahotanni daga ofishin hukumar WHO dai sun ce kasashen Turai 4 da suka hada da Albania, Burtaniya, Jamhuriyar Czech  da Girka, ya zuwa yanzu duk sun gaza kai bantensu a batun yaki da cutar kyanda.

 

Ofishin hukumar ya ja kunnen nahiyar Turai cewa ya zuwa yanzu ana samun koma baya daga ci gaban da ake ganin ta samu wajen fatattakar cutar.

 

Cutar kyanda dai ta kashe mutane 37 a nahiyar Turai daga  watan Janairu zuwa Yuni na wannan shekara ta 2109.

 

An kuma samu bullar cutar da kaso 80% a wasu kasashen Turai guda 4 da suka hada da Ukraine, Kazakhstan, Georgia da Rasha.

 

Yawan bullar cutar ya linka a nahiyar Turai a ”yan shekarun nan daga 5,000 a shekarar 2016 zuwa 26,000 a shekarar bara waccan ta 2017 sannan ya yi linkin-ba-linkin a shekarar bara ta 2018 ya zuwa 84,000.

 

Hukumar kula da lafiya ta duniya ta rawaito cewa samun sake bullar cutar a nahiyar Turai ba zai rasa nasaba da yadda hukumomin kula da lafiya suka yi biris da karade yankunan da al’ummomi suke ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply