Home Lafiya Cutar Lassa Fever ta bulla jihar Kaduna

Cutar Lassa Fever ta bulla jihar Kaduna

90
0

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar a ranar Asabar cewa cutar Virus ta Lassa Fever ta kama wani mutum  a Karamar Hukumar Chikun kuma gwamnati na ci gaba da ba shi magani a wata cibiya ta musamman da ke cikin garin Kaduna.

Wata sanarwa da Kwamishinan Lafiya na jihar Dokta Amina Mohammed-Baloni ta fitar ta ce mutumin da ya kamu da cutar yana da kimanin shekaru 36. Sai dai ta bukaci da jama’a su kwantar da hankulansu. Ta ce gwamnati ta samar da kayayyakin gwaji da kula da wannan cuta a asibitocin jihar. Kuma ya zuwa yanzu jami’an kiwon lafiya za su rinka sa ido sosai ga jama’an da ke zuwa asibiti don tabbatar da an hana yaduwar cutar mai saurin kisa.

Gwamnatin kuma ta bukaci jama’a da su rinka kula da tsaftar jiki da daukar matakan kariya daga kamuwa da cutar ta Lassa Fever. Ta ce tana kira ga jama’a duk wanda ya alamun wani ya kamu da cutar ya sanar da wani jami’in kiwon lafiya na karamar hukuma mafi kusa da shi ko kuma a kira wannan lambar waya da aka ware domin karbar korafe-korafe a kan Lassa Fever.

A ‘yan kwanakin nan ne daio Lassa Fever din ta bulla a jihar Kano, inda kawo yanzu rahotanni suka ce ta yi sanadin mutuwar mutane da dama.

 

Don karanta cikakkun hanyoyin da ake kare kai daga Lassa Fever sai a latsa wannan link din daga jaridar The Guardian ta harshen tutranci.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply