Hukumar kula da barkewar cutuka ta Nijeriya ta ce yanzu haka cutar zazzabin Lassa ta kashe mutum 185 a cikin shekarar 2020.
A makon da ya gabata ne dai aka ruwaito yawan wadanda suka mutu sakamakon cutar ya kai 176.
Saidai a bayanan halin da ake ciki game da cutar da hukumar ta wallafa a shafin ta na Intanet, NCDC ta ce yawan wadanda suka kamu da cutar yah aura daga 932 a makon da ya gabata zuwa 951 a wanna makon da muke ciki wanda shi ne na 13 tun bayan barkewar cutar.
Tun a farkon shekarar nan dai ne Nijeriya ke yaki da wannan cuta da itama aka bayyana ta a matsayin annobar duniya.
