Home Labarai Cutar Lassa ta yi wa jihar Bauchi kome

Cutar Lassa ta yi wa jihar Bauchi kome

113
0

Ya zuwa yanzu an tabbatar da mutum 22 da suka kamu da cutar farar masassara (yellow fever), inda mutum 6 kuma suka kamu da cutar Lassa a jihar Bauchi.

Shugaban sashen lafiya na jihar Bauchi Rilwanu Mohammed ya bayyana hakan ajiya yayin tattauna wa da shi ta wayar salula, ya ce cutar ta farar masassara ta yadu ne a yankin Miya da ke karamar hukumar hukumar Ganjuwa inda ya zuwa yanzu an tabbatar da samuwarta a jikin mutum 22 cikin mutum 63 da aka yi wa gwaji.

Ya kuma bayyana mutuwar mutum 2 a satin da ya gabata sakamakon cutar, wanda ya zuwa yanzu an samu mutuwar mutane 10 kenan tun bayan bullar cutar a jihar.

Yayinda ya tabbatar da samuwar cutar ta Lassa a yankin karamar hukumar Toro da Tafawa Balewa inda mutum 6 ke dauke da ita.

Ya kara da cewa ya zuwa yanzu, anyiwa Masu hidimar kasa (NYSC) 986 allurar rigakafi tare da ma’aikansu saboda yanda sansanin nasu yake makwabtaka da karamar hukumar ta Ganjuwa inda cutar ta bulla.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply