Home Lafiya Cutar shanyewar jiki za ta kashe mutane miliyan 5 da rabi

Cutar shanyewar jiki za ta kashe mutane miliyan 5 da rabi

40
0

Masana da kwararrin likitoci sun fara gargadi da aikin wayar da kai ga mutane dangane da yadda Cutar shanyewar baren jiki ke kara yawa da yaduwa a cikin al’umma.

Masanan irin su Dr. Auwal Ahmed wani kwararren likita a Sokoto na daya daga cikin likitocin da ke fafutukar wayar da kan al’umma kan wannan cuta ya ce ana samun mutum guda da ke dauke da wannan cuta a duk cikin mutum hudu a Nijeriya.

Baya ga shan sigari da hawan jini da suka zama manyan abubuwan da ke haifar da wannan cutar, wani bincike da kwararri suka yi a Asibitin koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato sun gano yawan shekaru na haifar da wannan cuta musamman daga 40 zuwa 70 kana da kuma uwa uba rashin motsa jiki.

Bincike ya nuna aƙalla mutum miliyan 5 da rabi ne cutar za ta iya kashewa a faɗin duniya.

A arewacin Nijeriya rashin kayan aiki da talauci na daga cikin abubuwan da ke ta’azzara Cutar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply