Home Labarai Da ɗumi-ɗumi: Majalisar dattawa ta amince da naɗin tsaffin hafsoshin tsaro matsayin...

Da ɗumi-ɗumi: Majalisar dattawa ta amince da naɗin tsaffin hafsoshin tsaro matsayin jakadu

49
0

Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da naɗin tsohon babban hafsan sojin Nijeriya Tukur Buratai, tsohon babban hafsan tsaro Gabriel Olanisakin, tsohon babban hafsan sojin sama Ibok Ibas da tsohon babban hafsan sojin ruwa Abubakar Sadique a matsayin jakadu.

Majalisar ta amince da naɗin ne a zamanta na yau biyo bayan rahoton da kwamitin wucin gadi da zai tabbatar da naɗin nasu ya gabatar.

A makonnin baya ne dai shugaba Buhari ya aike da sunayensu a gaban majalisa domin neman amincewarta a naɗa su jakadun ƙasar, kwanaki kaɗan bayan ajiye aikinsu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply