Tattalin arziƙin Nijeriya ya sake durƙushe wa karo na biyu a cikin shekara biyar bayan koma baya da ma’aunin ƙayyade tattalin arziƙin ya samo sau biyu a jere.
A ranar Asabar hukumar ƙididdiga ta Nijeriya NBS, ta ce tattalin arziƙin ya fuskanci koma baya da kashi 3.62% a zango na uku na shekarar 2020.
Durƙushewar tattalin arziƙin na wannan shekara wanda annobar COVID-19 ta janyo dai, ya fi wanda ƙasar ta fuskanta a shekarar 2016 muni.
