Home Labarai Da da uba na sana’ar wiwi a Kano

Da da uba na sana’ar wiwi a Kano

315
0

Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta ce ta yi nasarar cafke wani matashi dan kimanin shekaru 21 mai suna, Kabiru Mahmud tare da dauri 49 na tabar wiwi.

Jaridar Kano Focus ta rawaito cewa ‘yansandan sun yi nasarar kama Kabir Mahmud ne a Unguwar Danbure ta Gadonkaya inda zai kai ta zuwa gidansa.

Kakakin rundunar ‘yansanda ta jihar, Abdullahi Kiyawa ya ce rundunarsu ta samu wani rahoton sirri dangane da wannan matashi inda aka labarta wa jami’ansu cewa buhun da matashin ke dauke da shi tabar wiwi ce cikinsa.

Sai da Matashin ya bayyana wa jami’an ‘yansandan cewa, mahaifinsa ya shafe kusan shekaru ashirin yana harkar sayar da tabar wiwi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply