‘Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sake kai wa ayarin Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum hari a kokarinsa na shiga duba ’yan gudun hijira a Baga.
Bayanan da DCL Hausa ta tattaro na nuna cewa a Asabar din nan, da dagawar hantsi aka kaddamar da harin a dai-dai kauyen da ake kira Kwayamti da ke da nisan kilomita 60 daga Maiduguri. Sai dai kuma rashin sabis na salula a wurin ya hana fitar labarin har sai a daren Asabar wayewar garin Lahadin nan.
A sakamakon harin dai sojoji bakwai sun rasa rayukansu, ya yin da dan sintiri na civilian JTF guda daya shi ma ya sadaukar da rayuwarsa.
Labarai Masu Alaka: Boko Haram ta sake kai wa tawagar Zulum hari
“Muna rokon a gayyato sojin Chadi su yaki Boko Haram” – Zulum
Boko Haram: Gwamna Zulum ya tsallake rijiya da baya
DCL Hausa ta rawaito cewa dai babu wani abu da ya samu Gwamna Zulum domin tun farko shi an dauke shi a jirgin sama zuwa Baga.
Wannan shi ne karo na hudu a cikin wannan shekarar da ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne ke kai wa ayarin gwamna Zulum hari a duk lokacin da ya yi yunkurin shiga garin Baga domin duba yanayin tsaro da kuma ‘yan gudun hijira a garin da ke dab da tafkin Chadi. Sai dai har yanzu Boko Haram ba ta fito ta dauki alhakin kai harin ba.
