Home Kasashen Ketare Da Dumi-Dumi: An sanar Bazoum ya lashe zaben Nijar

Da Dumi-Dumi: An sanar Bazoum ya lashe zaben Nijar

20
0
Bazoum Mohammed dan takarar jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya

DCL Hausa ta samu labarin cewa yanzu-yanzu nan ne hukumar zabe ta kasar Nijar CENI ta bayyana sakamakon zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka gudanar a ranar Lahadin nan da ta gabata.

Dan takarar jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki ne dai Malam Bazoum Mohamed ya yi nasarar lashe zaben kamar yadda hukumar zaben ta bakin shugabanta maître Issaka Souna ta sanar a hedkwatar ta da ke a babban birnin Yamai.

Bazoum din dai ya yi nasarar lashe zaben ne da kuri’u 2,501,459 adadin da ya kai sama da kaso 55 da cikin 100, yayin da abokin hamayyarsa na jam’iyyar RDR Tchanji Alhaji Mahaman Ousman ya samu kuri’u 1,985,756 adadin da ya kai kaso 44 da ‘yan ka cikin dari.

A tsarin mulkin kasar dai duk wanda ya yi nasarar lashe sama da kaso 50 cikin 100 na kuri’un da aka kada, shi ne ya cinye zaben ko a zagaye farko ko a na biyu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply