Home Sabon Labari Ana zullumin an yi garkuwa da daliban Islamiyya masu yawa a Dandume,...

Ana zullumin an yi garkuwa da daliban Islamiyya masu yawa a Dandume, Katsina

10073
0

Rahotannin da ke zuwa ma DCL Hausa sun ce ana zullimin ‘yan bindiga sun yi garkuwa da daliban makarantar Islamiyya a karamar hukumar Dandume a ranar Asabar din nan da daddare.

Jaridar Katsina Post ta ce wakilinta na yankin ya sanar mata cewa daliban na garin Mahuta, Dandume an yi garkuwa da su ne kan hanyarsu ta dawo wa daga Maulidi daga wani kauye da ake kira Unguwar Al-kasim. Kawo yanzu dai ba a kai ga sanin adadin daliban Islamiyyar da ake zullimin an kwasa din ba.

Kakakin ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isa ya ce yana halartar wani taro a wajen jihar Katsina a saboda haka ba zai iya cewa wani abu ba a kan wannan farmakin.

 

Labari mai alaka:

SABON LABARI:’Yan sandan Katsina sun kwato ɗaliban Islamiyya 84 da aka sace

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply