Da safiyar yau Lahadi ne rundunar yansanda jihar Nassarawa ta tabbatar da yin garkuwa da sakataren gwamnatin jihar Jibrin Okaku Giza.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Nasarawa, Emmanuel Bola Longe ne ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce tuni aka fara binciken wadanda ke da hannu wajen aikata wannan lamari.
