Home Labarai Da dumi-dumi: APC ta lashe zaben cike-gurbi na Bakori

Da dumi-dumi: APC ta lashe zaben cike-gurbi na Bakori

215
0

Jam’iyyar APC mai mulki ta lashe zaben cike gurbi da ya gudana na dan majalisar dokoki jihar Katsina mai wakiltar karamar hukumar Bakori da ke jihar.

Babban baturen zabe Prof A.D Kankiya da ya ayyana Dr Ibrahim Kurami bayan tattara sakamakon zaben a Bakori, yace APC ta samu yawan kuri’u 20,444.

Yace PDP ce ta zo ta biyu a zaben da yawan kuri’u 11,356.

A ranar 11 ga watan Mayun, 2020 ne Allah Ya karbi ran dan majalisar dokoki mai wakiltar karamar hukumar Bakori Abdulrazar Isma’il Tsiga bayan rashin lafiya.

A baya dai, hukumar zabe ta INEC ta saka 31 ga watan Oktoba domin gudanar da zabukan cike gurbin, sai dai, zanga-zangar EndSARS ta kawo tsaiko har aka daga ya zuwa 5 ga watan Disamba, 2020.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply