Kulob din Arsenal na kasar Ingila ya Kori mai horas da kungiyar dama illahirin masu taimaka masa a kungiyar.
Rahotanni sun ce rashin nasarar da kulob din Arsenal din ya yi a ranar Alhamis a wasan da aka buga tsakaninsa da kungiyar Entracht Frankfurt shi ne babban dalilin da yasa kulob din ya sallami Emery Unai.
