Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya bude iyakokin kan tudu na kasar guda hudu.
Ministar Kudi Zainab Ahmed ta sanar bayan taron majalisar zartaswar Nijeriya a wannan Laraba.
Iyakokin da aka bude yanzu sun hada da Seme da ke kudu maso yammacin Nijeriya da
Illela a Sokoto da Maigatari ta Jigawa da kuma Mfun da ke kudu maso kudu.
Zainab ta ce nan da 31.12.2020 za a sanar da bude sauran iyakokin kasar. Sai dai Zainab Ahmad ta ce har yanzu takunkumin hana shigo da shinkafa na aiki.
