Home Labarai Da dumi-dumi: Burin ASUU ya cika, an cire su daga tsarin IPPIS

Da dumi-dumi: Burin ASUU ya cika, an cire su daga tsarin IPPIS

500
1

Bayan kwashe lokaci mai tsawo ana tattaunawa tsakanin gwamnatin Nijeriya da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU, daga karshe gwamnatin ta amince da cire su daga sabon tsarin albashi na IPPIS.

Gwamnatin ta kuma amince za ta biya malaman jami’o’i albashin su na watannin Fabrairu zuwa Yuni da tsohuwar hanyar da ta saba biyansu sabanin IPPIS da suka ki amincewa da ita.

Daily Trust ta ce wannan na daga cikin yarjeniyoyi da dama da aka cimmawa a ya yin taron da ya shafe sa’o’i 7 ana gudanarwa tsakanin wakillan gwamnatin Nijeriya karkashin jagorancin Chris Ngige, ministan kwadago da shugabannin ASUU karkashin jagorancin shugabansu Biodun Ogunyemi.

Da ya ke karanta takardar bayan taron, Chris Ngige yace gwamnati ta kuma ba da damar a yi wa malaman jami’o’in karin daga abin da suke samu daga Naira bilyan 30 zuwa bilyan 35.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

  1. Gaskiya karda gomnatin nageriya tabamu kunya acekamar asuu zasusa saitayi abu dole baba buhari yagyara wannan abundakefaruwa akansa saboda waje mutane kegani suke abundasuka gadama

Leave a Reply