Home Sabon Labari Da dumi-dumi: kotu ta rushe masarautu 4 da gwamna Ganduje ya kirkira...

Da dumi-dumi: kotu ta rushe masarautu 4 da gwamna Ganduje ya kirkira a Kano

93
0

Abdullahi Garba Jani

Babbar kotu a jihar Kano ta rushe masarautu 4 da sarakunansu da gwamnatin jihar Kano ta kirkiro.

A ranar 8 ga Mayun, 2019 ne gwamna Abdullahi Ganduje ya zartas da hukuncin kafa karin masarautu 4 a Rano, Bichi, Karaye da Gaya.

Majiyoyi na kusa-kusa sun tabbatar da gwamna Ganduje ne ya assasa wannan dokar kafa karin wadannan masarautu kuma ya gabatar wa majalisar dokokin jihar.

Da ya ke yanke hukunci a zaman kotun a ranar Alhamis, alkalin, kotun Mai shari’a Usman Na’Abba, ya ce majalisar ta yi karan-tsaye ga kundin tsarin mulkin kasa na 1999 da ya ba majalisar damar Samar da dokoki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply