[cmsmasters_row data_width=”boxed” data_padding_left=”3″ data_padding_right=”3″ data_top_style=”default” data_bot_style=”default” data_color=”default” data_bg_position=”top center” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_size=”cover” data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_padding_top=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_shortcode_id=”dcx8cl09n”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_bg_position=”top center” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_size=”cover” data_border_style=”default” data_animation_delay=”0″ data_shortcode_id=”vr9ixjiinq”][cmsmasters_text shortcode_id=”xmnodjb6z” animation_delay=”0″]
An dage taron da shugabannin kungiyar kwadigo suke da gwamnatin Nijeriya zuwa yau Laraba domin a bayar da dama ga kowane bangare ya shirya wa amincewa da dan uwansa.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN- ya ruwaito wani babban jami’i a kungiyar kwadigo ta NLC wanda bai so a ambaci sunansa ba, yana cewa kungiyoyin kwadigo sun sassauto da bukatar su. A yanzu sun amince gwamnati ta kara kashi 25 cikin dari na albashi ga ma’aikatan da ke matakin albashi na 7 zuwa 14 sabanin kaso 29 da suka nema da farko. Kazalika sun amince a yi karin kaso 20 maimakon 24 da suka nemi a karawa ma’aikatan da ke matakin albashi na 15 zuwa 17.
Mataimakin shugaban kungiyar NLC Comrade Amaechi Asugwuni ya shaida wa yan jarida a Abuja a ranar talata da daddare cewa taron da suka yi da gwamnati na ranar Talatar nan bai samu ya cimma matsaya ba. A don haka ya zama wajibi su dage taron zuwa ranar Laraba da misalin karfe 2 na rana.
Comrade Amaechi ya ce ya ga alamun gwamnati da gaske ta ke wurin biyan bukatun ma’aikata. Sai dai bai ce komai ba dangane da ko za a fara yajin aiki a ranar Laraba kamar yadda aka tsara ko kuma a’a.
[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]
