Home Labarai Da Dumi-Dumi: Sojoji sun kwato garin Marte daga Boko Haram

Da Dumi-Dumi: Sojoji sun kwato garin Marte daga Boko Haram

29
0

Bayan wa’adin awanni 48 da babban hafsin sojin kasa na Nijeriya, Ibrahim Attahiru ya bayar, dakarun sojojin sun yi nasarar kwato garin Marte daga hannun ‘yan ta’addar Boko Haram.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai Attahiru, ya ba da wa’adin awanni 48 don sojoji su fatattaki ‘yan ta’adda daga Marte da ma kauyukan da ke kusa da su, da suka hada da Kirenowa, kirta, Wulgo, Chikingudo a jihar ta Borno.

DCL Hausa ta ba da labarin yadda ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka kwace iko suka kuma hallaka sojoji yayin wata arangama.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply