Home Sabon Labari DA DUMI DUMI: Sulhun Gwamnan Katsina ya fara aiki, kidinafas sun sako...

DA DUMI DUMI: Sulhun Gwamnan Katsina ya fara aiki, kidinafas sun sako mata 10

67
0

[cmsmasters_row][cmsmasters_column data_width=”1/1″][cmsmasters_text]

Zaharaddeen Umar Dutsen-Kura

 

Matan su 10 anyi kidinafin dinsu kwanaki goma sha shida da suka wuce a kauyen Shimfida na Karamar Hukumar Jibia lokacin da suke kokarin komawa kauyensu daga garin Jibia. Cikinsu akwai mace mai shayarwa da kuma jariri dan watanni hudu.

Wasu daga cikin matan da kidinafas suka sako wa gwamnati a jihar Katsina

Acewar mai magana da yawun Sakataren Gwamnatin Katsina, Abdullahi Aliyu Yar’adua sako matan ya biyo bayan kokarin da gwamnatin jihar Katsina na baya-bayan nan inda ta yi wa kidinafas da sauran masu aikata laifi tayin yi musu afuwa da sulhu domin tabbatar da zaman lafiya a yankunan karkarar jihar Katsina. Dalilin ke nan da ya sa a dazu da rana kidinafas din suka sako matan kuma a kawo su ofishin Gwamnan jiahr Katsina.

Abdullahi ya ce kidinafas sun amince su sako wadannan mata bayan da gwamna Masari ya umarci a sako wasu ‘yan uwansu, domin tabbatar wa da duk wani mai tada zaune a Katsina cewa da gaske ya keyi a wannan sabon yunkurin na yin sulhu da afuwa.

Matan ke nan a lokacin da suke ganawa da Gwamna Masari a cikin ofishinsa

A ‘yan kwanakin nan dai Gwamna Aminu Bello Masari da Sakataren Gwamnati Mustapha Muhammad Inuwa da sauran jami’an gwamnati sun ba zama cikin dazazzuka a kananan hukumomi 8 da ke fuskantar matsalar tsaron don tattaunawa da masu aikata laifuka. A yanzu da aka fara ganin an sako mata 10 daga hannun kidinafas, ana fatan sulhu da afuwan za su tabbata kuma su dore kamar yadda ake ganin tasirinsu a jihar Zamfara.

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply