Home Labarai Da Dumi-Dumi: ‘Yan bindiga sun shiga jami’ar ABU, sun yi awon gaba...

Da Dumi-Dumi: ‘Yan bindiga sun shiga jami’ar ABU, sun yi awon gaba da mutane

268
0

Sanarwar da Daraktan Sashen Yada Labarai na jami’ar Ahmadu Bello Zaria Malam Auwalu Umar ya fitar a yammacin Litinin din na cewa a safiyar Litinin din da misalin karfe 12.50 na dare masu garkuwa da mutane suka shiga gidajen malaman jami’ar ABU da ke Samaru inda suka dauki wani ma’aikacin jami’ar da matarsa da kuma ‘yarsa.

Sanarwar wace jaridar DCL Hausa ta samu a shafin wayar da kan jama’a na jami’ar a Facebook ta ce da ‘yan sanda suka bi sawun ‘yan bindigar sun yi nasarar kwato matar malamin da kuma ‘yarsa sai dai shi kuma sun gudu da shi. Jami’ar ABU din ta ce tuni ta sanar da hukumomin da suka dace.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply