Daga Mu’awiyya Abubakar Saddiq
Bayanan da wakilinmu ya tattaro sun nuna cewa jami’an hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da hana karya tattalin arzikin kasa a Nijeriya sun mamaye gidan tsohon gwamna Abdul Aziz Yari da ke a mahaifarsa a garin Talatar-Mafara a jihar Zamfara.

Wani mazaunin kusa da gidansa wanda ya dauki hotunan ya tura wa wakilinmu ya shaidawa DCL Hausa cewa jami’an EFCC sun isa gidan tsohon gwamnan tun bayan magaribar ranar Lahadi.

Jami’an dauke da cikakkun kayan su na aiki sun yi rashin sa’a domin bayanai sun nuna cewa ba su iske tsohon gwamnan ba.

A gefe guda a yayinda ayarin EFCC ya yiwa gidan Abdul Aziz Yari kawanya, wasu matasa sun fito suna yiwa jami’an ihu, abin da ya kai ga jami’an EFCC din harba bindiga a sama don su tarwatsa su.
Zargin Almundahana
Kawo yanzu dai jamian EFCCin ba su kai ga sun yi bayanin abin da ya kai su gidan tsohon gwamnan ba, amma a watan Yuni na wannan shekarar shugaban kwamitin karbar gwamnati Alhaji Ibrahim Wakkala ya yi zargin cewa Abdul Aziz Yari ya kwashe kudin jama’ar jihar Zamfara sama da Naira Bilyan 250 ba tare da yayi aikin komi ba. A baya an zargi hukumar EFCC da kin waiwayar wannan zargi. Sai kuma ga shi yanzu kwatsam an gansu a gidan tsohon gwamnan.

Gabadai-gabadai EFCC aikinku na kyau sosai, Allah ya baku sa’ar kwato kudin al-umma hannun barayin Gwamnati.